Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Bukaci 'Yan Tawayen Liberiya Da Su Sako Ma'aikatan Jinya - 2002-06-22


Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta roki 'yan tawaye a Liberiya, da su sako ma'aikatan jinya guda biyar da suka sace lokacin da ake gwabza kazamin fada tsakaninsu da sojojin gwamnati.

Wani kakakin MDD, Kris Janowski, ya ce a ranar alhamis da sanyin safiya 'yan tawayen na Liberiya suka kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira na Sinje dake arewa maso gabas da Monrovia, babban birnin kasar, inda suka sace wadannan ma'aikatan jinya.

Jami'in ya ce 'yan tawaye sun kuma sace wasu kayayyaki na MDD, sannan suka fatattaki ma'aikatan agaji su 60 'yan kasar tare da 'yan gudun hijira su kimanin dubu 11.

Wani kwamandan 'yan tawaye dake kiran kansa "Janar Skeleton", ko janar kashi a Hausance, ya shaidawa hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta hanyar sadarwar rediyo samfurin over-over, cewa wadannan ma'aikatan jinya suna nan lafiyarsu kalau, kuma za a dauke su zuwa wata tungar 'yan tawaye dake kusa da kasar Guinea.

Wannan sansani dake kusa da bakin iyakar Liberiya da Saliyo, ya shafe makonni uku ba ya samun kayan agaji daga waje a saboda karuwar fadace-fadace.

XS
SM
MD
LG