Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Taron Kolin OAU Ya Ce Babu Halaltacciyar Gwamnati A Madagascar - 2002-06-22


Wani dan karamin taron kolin da kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka ta OAU ta kira a Ethiopia domin warware rikicin siyasar da aka yi watanni shida ana fama da shi a Madagascar, ya zartas da cewa babu halaltacciyar gwamnati a wannan tsibiri.

Sanarwar da aka bayar yau asabar a karshen wannan taron koli, ya ce bai kamata a kyale gwamnatin Didier Ratsiraka ko ta Marc Ravalomanana ta wakilci kasar Madagascar a wajen taron kolin kungiyar OAU da za a yi cikin wata mai zuwa a birnin Durban, a Afirka ta Kudu ba.

Sanarwar ta ce ba za a kyale wani ya hau kan kujerar Madagascar a cikin kungiyar OAU ba har sai an kafa halaltacciyar gwamnati a kasar.

Mr. Ratsiraka, wanda ya halarci taron na birnin Addis Ababa, ya amince da wannan kuduri na kungiyar OAU. Mr. Ravalomanana bai je shi kasar Ethiopia wurin taron ba, sai dai wakilansa dake can sun bayyana rashin yarda da wannan shawara ta kungiyar OAU.

Sanarwar ta kuma yi kira ga abokan gabar siyasar na Madagascar ad su rushe kungiyoyin 'yan bangar da suka kakkafa, da shingayen tare hanyoyin mota, sannan su kawo karshen duk wani tashin hankali.

Kasar Madagascar dai ta dare gida biyu tun zaben shugaban kasa na watan Disamba da ake gardamar sakamakonsa. Mutane akalla saba'in sun mutu a tashin hankali tun watan Fabrairu.

XS
SM
MD
LG