Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Zata Nemi Kaiwa Inda Wata Kasar Afirka Ba Ta Taba Kaiwa Ba A Fagen Tamaula - 2002-06-22


'Yan wasan Senegal zasu yi kokarin kaiwa ga matakin da babu wata kasar Afirka da ta taba kaiwa, idan sun gwabza yau asabar da 'yan wasan Turkiyya a rana ta biyu ta wasannin kwata-fainal a wajen gasar cin kofin tamaula ta duniya.

A duk tsawon tarihin wannan wasa, babu wata kasar Afirka da ta taba kaiwa ga wasan kusa da na karshe. Idan 'yan Senegal suka samu nasarar yin waje-rod da Turkiyya, zasu fuskanci 'yan wasan kasar Brazil a wasan kusa da na karshe. A jiya Jumma'a 'yan Brazil din suka doke Ingila da ci 2-1 a wasan farko na kwata-fainal.

A daya wasan kwata fainal na yau asabar kuma, Koriya ta Kudu mai masaukin baki, zata gwada karfin damtsenta, ko na guiwarta da 'yan wasan Spain. Kafin bana, sau 14 Koriyar tana buga wasannin cin kofin duniya, kuma sau 14 tana shan kashi. A bana, ta lashe wasanni uku tayi kunnen doki a guda ya zuwa yanzun nan.

Wadda ta samu nasara a tsakanin Koriya ta Kudu da Spain kuma, zata gamu da Jamus, wadda a jiya Jumma'a tayi wa Amurkawa ci daya mai ban haushi.

An ce hankulan jama'a a nahiyar Afirka baki daya ya koma kan 'yan wasan senegal, wadanda zasu fara wasan nasu da misalin karfe 12 da rabi na rana agogon Nijeriya.

XS
SM
MD
LG