Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FBI Tayi Gargadi Game Da Hare-hare Kan Wuraren Ibadar Yahudawa - 2002-06-22


Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya ta Amurka, FBI, ta shawarci hukumomin tsaro dabam-dabam da su zauna da shirin cewa zai yiwu 'yan ta'adda su kai hare-hare ta yin amfani da motocin jigilar man fetur a zaman makami.

Hukumar ta fada jiya Jumma'a cewar ta samu bayanan cewar watakila 'yan ta'adda suna shirin yin amfani da tankokin na mai domin kai hare-hare kan unguwani da wuraren ibadar yahudawa a nan Amurka da kuma wasu kasashe.

Amma kumka hukumar ba ta ce ga wani takamammen wurin da za a kai wa hari cikin wannan sanarwar tata ba.

A cikin 'yan makonnin nan, hukumar FBI ta bada takardun sanarwa masu yawa a wani yunkurin rigakafin hare-haren ta'addanci.

XS
SM
MD
LG