Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani madugun Musulmi 'Yan Tawaye A Kasar Philippines - 2002-06-22


Rundunar sojojin kasar Philippines ta ce ana kyautata zaton an kashe wani madugun kungiyar Musulmi 'yan tawaye ta Abu Sayyaf, a bayan wata arangamada sojojin gwamnati.

Rundunar sojan ta ce zaratan sojojin Philippines sun yi amfani da na'urorin bin sawun mutane da na sadarwa na Amurka wajen farauto Abu Sabaya a lokacin da yake tafiya cikin wani jirgin kwale-kwale jiya Jumma'a a dab da tsibirin Mindanao.

Rundunar sojan ta ce an harbi Abu Sabaya, kuma gawarsa ta nutse cikin teku. Shugaba Gloria Arroyo ta Philippines ta ce mayakan ruwa suna neman gawar a cikin teku.

Shugaba Bush na nan Amurka ya ce kashe Abu Sabaya da aka yi a bisa dukkan alamu, ya nuna cewa kasashe masu kwadayin 'yancin walwala zasu iya yin aiki tare su kuma samu nasara wajen yakar ta'addanci.

Jami'an Amurka sun ce kungiyar 'yan tawaye ta Abu Sayyaf tana da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta al-Qa'ida.

XS
SM
MD
LG