Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Tana Binciken Kisan Da Sojojinta Suka Yi  Jiya Jumma'a A Jenin - 2002-06-22


Rundunar sojojin Isra'ila ta ce tayi kuskure a lokacin da ta kashe Falasdinawa akalla uku, cikinsu har da yara kanana guda biyu, a wata kasuwa dake garin Jenin a yankin Yammacin kogin Jordan.

Rundunar sojan ta ce tana binciken lamarin na jiya Jumma'a.

Isra'ila ta ce sojojinta sun harba kwanson nakiyoyin tanka guda biyu a kan mutanen da suke zaton wai masu karya dokar hana yawo ne da suka nufo kansu.

Amma kuma Falasdinawa shaidu na gani da idanu sun ce Falasdinawan sun yi zaton an dage dokar hana yawon.

Har ila yau a jiya Jumma'ar, firayim minista Ariel Sharon da majalisar zartaswar tsaronsa sun sake jaddada shawararsu ta sake mamayewa tare da rike yankunan Falasdinawa har sai an kawo akrshen hare-hare a kan Isra'ila.

A nan Washington kuma, shugaba Bush ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta daga hare-haren Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG