Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya ce a shirye yake ya gwabza yaki da kasar Indiya kan yankin nan na Kashmir, duk da matakan da hukumomin Indiya suka dauka cikin 'yan kwanakin nan na rage zaman tankiya tsakanin abokan gabar junan masu makaman nukiliya.
Janar Musharraf ya shaidawa gidan telebijin na Britaniya jiya asabar cewa makwabtan biyu sun yi kusan gwabza yaki kwanakin baya, amma kuma tankiya ta ragu a yanzu. Shi ma firayim minista Atal Behari Vajpayee na Indiya yayi irin wannan furuci ga mujallar Newsweek, inda ya ce abu kiris ya hanawa kasashen biyu gwabza yaki.
Janar Musharraf ya ce za a ci gaba da zaman tankiya har sai lokacin da Indiya ta janye sojojinta daga bakin layin nan da ya raba tsakanin kasashen biyu a Kashmir.