An jinkirta gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi da majalisun birane a kasar Kamaru saboda rashin tsari mai kyau, kuma a dalilin haka, shugaba Paul Biya ya kori ministan harkokin cikin gida.
Sa'a guda a bayan da aka bude rumfunan zabe jiya lahadi, shugaba Biya ya gabatar da wata dokar shugaban kasa da ta ce za a jinkirta zaben da mako guda a saboda matsalolin kayan aiki.
Rumfunan zabe da dama a Yaounde, babban birnin kasar, ba su samu kayan aiki ba.
A lokacin zaben majalisar dokoki na karshe da aka yi shekaru biyar da suka shige, 'yan adawa sun yi zargin cewa an tabka magudi mai munin gaske. A wannan karon ma, jam'iyyun adawa sun yi irin wannan argin, suna zargin gwamnati da laifin shirya 'yar ta-zarce.