Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Senegal Suna Bukukuwan Murna... - 2002-06-24


Al'ummar kasar Senegal suna ci gaba da bukukuwan murna, duk da cewa Turkiyya ta fitar da kasar daga cikin wasan neman cin kofin kwallon kafar duniya a ranar asabar.

Daruruwan mutane sun fantsama kan tituna suna waka suna hura hon na motocinsu. Shugaba Abdoulaye Wade ya yabawa kungiyar kwallon kafa ta kasar, yana mai fadin cewa sun daga darajar kasarsu suka sanya ta yin alfahari, suka kuma kawo mutunci ga nahiyar Afirka.

Shi kuma mai koyar da 'yan wasan na Senegal, Bruno Metsu dan kasar Faransa, ya ce 'yan wasan nasa suna nuna hali na hadin kai.

Ana sa ran cewa da yawa daga cikin shahararrun 'yan wasan kungiyar ta Senegal, cikinsu har da zakaran 'yan wasan kwallon kafa na nahiyar Afirka na 2001, El Hadj Diouf, zasu rattaba hannu kan sabbin takardun kwantaraki buga kwallo ma kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Turai. Da yawa daga cikin 'yan wasan, suna bugawa kulob-kulob na farfeshinal a Faransa.

A bana, Senegal ce kawai kungiyar Afirka da ta kai zagayen kwata-fainal a gasar cin kofin kwallon kafar duniya, kuma a tarihi ma, ita ce ta biyu kawai daga nahiyar da ta taba kaiwa ga wannan matsayi.

XS
SM
MD
LG