Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Falasdinawa Sun Yi Wa Shugaban Hamas Daurin Talala - 2002-06-24


Jami'an Falasdinawa sun ce 'yan sandansu sun yi wa shugaban kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas daurin talala, yayin da tankokin Isra'ila suka shiga cikin birnin Ramallah a Yammacin kogin Jordan.

Jami'ai suka ce an yi wa Sheikh yassin talala cikin gidansa dake birnin Gaza.

Wannan matakin ya zo a daidai lokacin da tankoki 25 na sojan Isra'ila suka shiga cikin Ramallah yau litinin da asubahi, garin Falasdinawa na shida da sojojin Isra'ila suka mamaye cikin 'yan kwanakin nan. Falasdinawa sun ce jirage masu saukar ungulu guda biyu na Isra'ila suna yin shawagi a samaniyar birnin, yayin da sojojin Isra'ila suka kewaye hedkwatar shugaban Falasdinawa Yasser Arafat.

A jiya lahadi sojojin Isra'ila suka mamaye garin Qalqilyah. Har ila yau Isra'ila ta sake mamaye garuruwan Bethlehem, Jenin, Nablus da kuma Tulkarm, inda jami'an Falasdinawa suka ce tankin Isra'ila ya harbe ya kashe wani dan sandan Falasdinawa.

Isra'ila tana saka dakarunta cikin damara, a bayan da a makon jiya majalisar zartaswar tsaron Bani yahudu ta yanke shawarar sake mamaye manyan biranen Falasdinawa na yankin Yammacin kogin Jordan har sai an kawo karshen hare-hare a kan Isra'ila.

XS
SM
MD
LG