Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Amince Da Marc Ravalomanana A Matsayin Shugaban Madagascar - 2002-06-27


Gwamnatin Amurka ta amince da Marc Ravalomanana a matsayin shugaban kasar Madagascar, bayan da tsibirin dake gabar tekun kudu maso gabashin nahiyar Afirka yayi fama da rikicin siyasar watanni shidda.

Gwamnatin Amurka za ta kuma saki kadarorin kasar Madagascar, wadanda ta dakatar tun a cikin watan disemba bayan zaben shugaban kasar da aka yi takaddama a kai.

Hukumomi a birnin Washington sun dauki wannan mataki ne a jiya laraba, ranar da Madagascar ta cika shekaru 42 da samun 'yancin kan ta daga kasar Faransa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, ya ce gwamnatin Amurka ta yanke wannan shawara ce bisa, hukumcin da babbar kotun tsarin mulkin kasar Madagascar ta yanke a karshen watan Afrilu cewa Mr. Ravalomanana ne ya lashe zaben, kenan ya kada dadadden shugaban kasar, Didier Ratsiraka.

A cikin watanni shiddan da suka gabata kasar Madagascar ta dare tsakanin abokan gabar. A kalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu a cikin tarzoma mai nasaba da rikicin siyasar.

XS
SM
MD
LG