Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadun Afirka Zasu Fara Taron Share fagen Kaddamar Da Tarayyar Kasashen Afirka - 2002-06-28


Jakadu daga kasashen Afirka sun fara taro domin tsara taron kolin kaddamar da sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka, wadda zata maye gurbin Kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka ta OAU wadda aka kafa shekaru 40 da suka shige.

Taron na yau Jumma'a da ake yi a birnin Durban mai tashar jiragen ruwa a Afirka ta Kudu, za a biyo bayansa da wani taron na ministocin harkokin waje, wadanda zasu rubuta kammalalliyar ajandar wannan taron. Shugabannin nahiyar zasu gana ranar 9 ga watan Yuli a birnin na Durban.

Mai rikon mukamin ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu, Zola Skweyiya, ya ce sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka ba zata zamo ci gaba kawai na kungiyar OAU ba, zata shimfida wata sabuwar gafaka ce wadda gwamnatocin kasashen Afirka zasu yi amfani da ita wajen auna kamun ludayin junansu a fannoni kamar na kare hakkin bil Adama.

Ya ce Tarayyar Kasashen Afirka zata maida hankalinta ga taimakawa wajen aiwatar da shirye-shiryen farfado da tattalin arzikin Afirka, kamar yadda yake kunshe cikin Sabon Shirin Kawancen Raya Kasashen Afirka.

Jami'in na Afirka ta Kudu ya ce ba kamar kungiyar OAU ba, sabuwar tarayyar zata kasance mai cikakkiyar dama da ikon takalar batutuwan tsaron zaman lafiya, tsaro da kuma tabbatar da dorewar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG