Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Kasashe Masu Arzikin Masana'antu A Canada - 2002-06-28


Shugabannin kasashen duniya amsu arzikin masana'antu dake ganawa a kasar Canada, sun kammala taron kolinsu tare da bayyana kwarin guiwa kan bunkasar tattalin arzikin duniya, da kuma bayyana kudurin yakar ta'addanci.

A cikin sanarwar da mai masaukin baki, firayim ministan Canada, Jean Chretien, ya bayar, shugabannin kasashen takwas da ake kira G-8, sun ce suna da kwarin guiwa game da karfin bunkasar tattalin arzikin kasashensu, da kuma bunkasar tattalin arziki a fadin duniya.

Shugabannin kasashe 7 da suka fi arzikin masana'antu sun yi alkawarin bada agajin kudi dala miliyan dubu 20 ga sabuwar membarsu ta cikon takwas din, watau kasar Rasha. Za a yi amfani da kudin domin taimakawa Rasha wajen kwance damarar makaman nukiliyarta tare da tabbatar da cewa ba su fada a hannun 'yan ta'adda ba.

Firayim minista Chretien na Canada kuma, ya bada sanarwar cewa kasashen masu arzikin masana'antu zasu goyi bayan agajin raya kasa ga Afirka. Sabuwar yarjejeniyar da aka cimma ta gabatar da tayin bada karin agajin da ba a fayyace ba, da kuma zuba jari a kasashen da gwamnatocinsu suka magance matsalar zarmiya da cin hanci, suka kuma rungumi akidar walwalar kasuwanci.

XS
SM
MD
LG