Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bukaci Sabon Shugaban Madagascar Da Yayi Kokarin Sasanta Al'ummarsa - 2002-06-28


Amurka ta yi kira ga sabon shugaban kasar Madagascar, Marc Ravalomanana, da ya ci gaba da aikin sasanta al'ummar kasar.

Cikin wata sanarwar da ta bayar jiya alhamis, fadar White House ta kuma yabawa shugabannin Afirka a saboda kokarin da suka yi na kawo karshen rikicin siyasar Madagascar.

Mr. Ravalomanana da Didier Ratsiraka, wanda ya jima yana mulkin Madagascar, duk suna ikirarin rike kujerar shugabancin kasar a bayan zaben shugaban kasa na watan Disamba da ake yin gardama a kai.

A karshen watan Afrilu, babbar kotun tsarin mulki ta Madagascar ta ayyana Mr. Ravalomanana a zaman shugaban kasa bayan da ta sake kidaya kuri'un.

A ranar laraba kuma, Amurka ta amince da shi a zaman shugaban kasar Madagascar har ma ta ce zata sako dukiyoyi da kadarorin Madagascar da ta rike.

XS
SM
MD
LG