Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Asabar Turkiyya Zata Yi Karon Batta Da Koriya Ta Kudu... - 2002-06-29


A yayin da ake shirin yin ba-ta-kashi a wasan karshe na cin kofin kwallon kafar duniya gobe (lahadi), a yau asabar Turkiyya da Koriya ta Kudu zasu bai wa hammata iska, a kwallance, domin tantance ko wacece zata buga kirjin cewa ita ce ta uku a wannan wasan da ya fi kowanne farin jini a fadin duniya.

Turkawa dai tuni sun yi waje-rod da daya mai masaukin baki, watau Japan. Watakila wannan zai zamo abin kashedi, ko kuma abin kara karfin guiwa ga 'yan Koriya ta Kudu, wadanda suka kawo wannan matsayin da babu wata kasar Asiya da ta taba kaiwa a fagen tamaular cin kofin duniya.

Koriya ta Kudu ita ce kasar farko wadda ba ta nahiyar Turai ba, da ta taba kaiwa ga wasan neman ta uku tun lokacin da Brazil ta doke Italiya a 1978. Mai koyar da 'yan wasan Koriya, Guus Hiddink, ya ce 'yan wasansa zasu zage damatsunsu su yi da gaske domin dadada wa miliyoyin masu goyon bayansu.

A gobe lahadi kuma, a birnin Yokohama a kasar Japan, 'yan wasan Brazil, wadanda wasu ke ganin sune gwanaye, zasu gwabza da Jamusawa, domin gano ko wacece zata iya buga kirjin cewa ita ce zakarar kofin kwallon kafar duniya a shekarar 2002.

XS
SM
MD
LG