Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Agaji Sun Ce Shirin Da Kungiyar G-8 Ta Gabatar Game Da Afirka Bai Wadatar Ba - 2002-06-29


Kungiyoyin agaji da masana tattalin arziki sun soki lamirin wani shirin bunkasa raya kasa a nahiyar Afirka wanda aka rattabawa hannu cikin makon nan a wurin taron kolin kasashe takwas mafiya arzikin masana'antu, koda yake shugabannin Afirka suna yabawa shirin.

Shugabannin Afirka da suka halarci wurin taron kolin a Canada sun bayyana shirin a zaman wani sabon babi a kawancen kasashe masu arziki da matalauta na duniya.

Amma kuma kungiyoyin agaji sun bayyana wannan shirin a zaman wanda bai wadatar ba, suna masu fadin cewa bai kai mizanin abinda nahiyar Afirka take bukata domin yakar talaucin da yayi mata kanta ba, da kuma cututtuka kamar kanjamau ko AIDS, da zazzabin cizon sauro, da kuma yunwa.

Wani dan rajin tallafawa Afirka, Neville Gabriel, ya rubuta sharhi cikin jaridar Guardian ta Afirka ta Kudu a jiya Jumma'a, inda ya ce wannan shiri na kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu yayi watsi da abubuwa na zahiri game da Afirka. Ya ce tattalin arzikin Afirka ba zai bunkasa ba yayin da kasashe masu arzikin masana'antu suke sanya faduwar farashin kayan amfanin gona a duniya ta hanyar bada sassaucin kudi mai yawan gaske ga manomansu, a can wani gefen kuma suna tilastawa kasashen Afirka da su cire irin wannan kudin sassauci.

A ranar alhamis, shugabannin kasashen da suka fi arzikin masana'antu a duniya sun yi alkawarin kara yawan agaji da jarurruka a Afirka, musamman ma a kasashen da suka kawar da cin hanci da rashawa, suka kuma aiwatar da sauye-sauyen shimfida tsarin tattalin arziki mai walwala.

XS
SM
MD
LG