Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Nemi Kamfanonin Amurka Su Ringa Nuna Da'a - 2002-06-29


Shugaba Bush ya soki lamirin manyan kamfanonin Amurka, a bayan da labari ya fito cewar wani kamfanin am ya shirga karya game da yawan kudaden da ya samu.

Mr. Bush ya fada jiya Jumma'a cewar yana da niyyar tabbatar da cewa ana yin aiki da dokokin da suka bukaci shugabannin manyan kamfanonin su ringa da'a.

Ya ce tilas manyan kamfanoni su fahimci cewa nauyi ne na tilas a kansu su ringa fadin gaskiya.

A farkon makon nan kamfanin wayar tarho an WorldCom ya bayyana cewa ya shirga karya ta hanyar kara kusan dala miliyan dubu hudu kan ribar zahiri da ya samu. A yanzu haka, kamfanin ya fara sallamar ma'aikata dubu 17 domin rage kudin da yake kashewa tare da tabbatar da cewa bai talauce ba.

A makon nan kuma, kamfanin Xerox mai kera na'urorin aiki a ofis ya ce ya gano kuskuren lissafin dala miliyan dubu biyu cikin kudin da ya samu. A farkon wannan shekara kuma, makeken kamfanin sarrafa makamashi na Enron ya talauce, inda dubun dubatan ma'aikatansa suka yi hasarar dukkan kudaden ritayarsu da na fensho da suka tara.

XS
SM
MD
LG