Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Ruwan Yaki Sun Yi Musanyar Wuta A Kusa Da Gabar Koriya - 2002-06-29


Jiragen ruwan yakin Koriya ta Arewa da ta Kudu sun yi musanyar wuta da bindigogi a dab da gabar yammacin yankin kasashen biyu na Koriya.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ya ce an raunata mayakan ruwansu guda biyar, kuma nan gaba kadan zasu bada cikakken bayanin abubuwan da suka faru.

Rahotanni a kasashen sun ce an yi wannan musanyar wuta ta dan kanakanin lokaci yau asabar a tekun Yellow Sea dake dab da tsakiyar zirin kasashen biyu.

An ce jiragen ruwan yaki guda biyu na 'yan Kwaminis sun yi rakiya tare da nuna hanya ma wasu jiragen ruwan kamun kifi na Koriya ta Arewa a cikin yankin ruwan Koriya ta Kudu kafin a fatattake su zuwa bayan layin da ya raba tsakanin kasashen biyu.

Babu wani takamammen abu da ya raba iyakar kasashen biyu na Koriya ta cikin teku, kuma Koriya ta Arewa tana gardamar yadda ake daukar iyakacin nasu.

XS
SM
MD
LG