Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bai Wa Alasanne Ouattara Takardar Shaidar Zama Dan Kasa - 2002-06-30


An bai wa tsohon firayim minista, kuma jagoran 'yan adawar Ivory Coast, Alassane Ouattara, takardar shaidar zamowa dan kasa, abinda ya kawo karshen mummunan rikicin da aka jima ana yi kan ko shi dan wace kasa ce.

Lauyan Malam Ouattara, Emammanuel Assi, ya fada jiya asabar cewa a yanzu dai bangaren shari'a na Cote D'Ivoire ya mikawa tsohon firayim ministan takardar shaidar zama dan kasa hannu da hannu.

Wannan labari ya zo a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben kananan hukumomi da yankuna a ranar 7 ga watan gobe na Yuli. Jami'ai sun damu kan cewa ci gaba da sabani game da batun ko Malam Alassane Ouattara dan wace kasa ce yana iya haddasa fitinar kabilanci a lokacin zaben.

Mutane akalla hudu sun mutu a wani tashin hankalin da aka yi cikin makon nan a garin Daloa dake tsakiyar kasar.

A shekarar 2000, kotun kolin Ivory Coast ta hanawa malam Ouattara tsayawa takara a zabubbuka na kasa saboda tababar da aka yi kan kasarsa ta asali. Wannan abu ya haddasa fada a tsakanin magoya bayan shugaba Layrent gbagbo da aka zaba da na 'yan adawa.

A karshen shekarar da ta shige, wani taron sasantawa na kasa da aka gudanar a Abidjan, babban birnin kasar, ya bada shawarar bai wa Malam Ouattara takardar zamowa dan kasa domin a samu zaman lafiya a kasar.

XS
SM
MD
LG