Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Moi Yana Son karin Lokaci Domin Shirya Sauye-Sauyen Tsarin Mulki - 2002-06-30


Shugaba Daniel Arap Moi na Kenya yayi kiran da a karawa majalisar dokoki wa'adi kan mulki, tare da shi kansa, ta yadda za a samu sukunin gudanar da zabe na gaba karkashin sabon tsarin mulkin da suke rubutawa a yanzu.

Shugaba Moi ya bayyana goyon bayansa ga wani shirin da jam'iyyarsa ta KANU ta gabatar na a dage zaben majalisar dokoki har sai an rubuta sabon tsarin mulki.

Shugabannin adawa sun ce shugaban yana neman da a jinkirta zabe ne kawai domin ya samu karin lokaci na zabo mutumin da yake son ya gaje shi.

A karkashin tsarin mulki na yanzu, tilas ne shugaba Moi ya sauka daga kan mulki a watan Janairu. yayi shekaru 24 yana mulkin kasar Kenya.

XS
SM
MD
LG