Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba A Ga 'Yan Kishin Falasdinu Cikin Ginin Da Isra'ila Ta Rushe Ba - 2002-06-30


Sojojin Isra'ila dake binciken kangon ginin hedkwatar majalisar mulkin kai ta Falasdinawa da suka rushe a Hebron, ba su ga alamar 'yan kishin Falasdinu su 15 da aka yi imanin sun buya a ciki ba.

Jami'an sojan Isra'ila sun ce tana yiwuwa mutanen sun sulale sun tsere kafin sojojin Isra'ila su dasa nakiya mai nauyin ton biyu su ragargaza ginin jiya asabar da sanyin safiya.

Mutane akalla 20 da ake nema sun mika kawunansu a bayan da sojojin Isra'ila suka kewaye hedkwatar ranar talata. Amma 'yan kishin Falasdinu su kimanin 15 sun ki yarda su mika kai.

Babban jami'in tsaron kai na Falasdinawa a yankin Yammacin kogin Jordan, Jibril Rajoub, ya ce yayi imanin babu kowa cikin hedkwatar a lokacin da Isra'ila ta tayar da wannan nakiya. Ya ce Isra'ila tana so ne kawai ta rushe wannan gini a saboda alama ce ta ikon majalisar mulkin kan Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG