Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil Da Jamus Zasu Yi Karon Batta... - 2002-06-30


Tsoffin zakarun kwallon kafar duniya Brazil da Jamus zasu yi gumurzu da juna yau lahadi a Yokohama a kasar japan, domin ganin ko wacece zata koma gida da kofin kwallon kafar duniya a wannan karon.

Za a fara wannan wasa da karfe 12 na rana agogon Nijeriya da Nijar, karfe 7 na safe agogon Washington DC.

Wannan shine karo na 7 da kowaccensu take bayyana a wasan karshe na neman cin kofin, amma kuma abin mamaki, ba su taba karawa da juna a wasan karshen ba.

Masu fashin bakin tamaula sun ce wasan yau dai, wasan gwajin damtse ne tsakanin 'yan wasan gaba masu kai farmaki na Brazil, da 'yan wasan baya masu tsaron gida na Jamus. Dan wasan Brazil mai suna Ronaldo, wanda ya fi kowa jefa kwallaye masu yawa a gasar ta bana, zai yi kokarin kalubalantar mai tsaron gida na Jamus, Oliver Kahn, wanda tun da aka fara wannan wasa, sau daya tak aka jefa kwallo cikin ragarsa.

Ana sa ran mutane miliyan dubu daya da dari biyar ne a fadin duniya zasu zauna domin kallon wannan wasa a akwatunan telebijin.

A jiya asabar dai, Turkiyya ta cire mai masaukin baki Koriya ta Kudu da ci 3-2, ta dauke matsayin ta uku. Turkiyya ta kuma yi wani abinda babu wanda ya taba yi cikin wannan gasa, watau ta jefa kwallo cikin dakika 11 tak da fara wasan.

Ana sa ran dubban 'yan kallo zasu tarbi 'yan wasan Turkiyya yau lahadi idan sun sauka a filin jirgin saman Istanbul.

A halin da ake ciki, jiya asabar miliyoyin 'yan Koriya ta Kudu suka fito kan tituna domin murnar irin nasarorin da 'yan wasansu suka samu a gasar cin kofin duniyar. Babu wata kungiya daga nahiyar Asiya da ta taba kaiwa ga wasan kusa da na karshe a duk tarihin gasar cin kofin kwallon kafar duniya.

XS
SM
MD
LG