Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Nace Kan Lallai Sai Falasdinawa Su Zabi Wasu Shugabannin Dabam - 2002-07-01


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce shugaba Bush ba zai ja da baya ba game da shawarar da ya yanke ta yin matsin lambar samar da sabbin shugabannin Falasdinawan da za su maye gurbin malam Yasser Arafat.

A lokacin da yake magana a jiya lahadi ta gidan telebijin na Amurka, Mr. Powell ya ce yanzu haka, gwamnatin Amurka ta bar magana da malam Yasser Arafat, sannan kuma ya ce babu wasu shirye-shiryen yin hakan nan gaba.

Mai bai wa shugaba Bush shawara a fannin tsaron kasa, Condoleezza Rice, ta ce babu abinda gwamnatin Amurka za ta iya yi ta ingiza matakin sulhun yankin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba, sai fa idan an samu wasu shugabannin Falasdinawan da za su dauki matakin magance ta'addanci.

Duk da haka dai shugabannin kungiyar PLO sun ce irin wannan suka game da shugabancin malam Yasser Arafat zancen banza ne. Wata sanarwar kwamitin zartaswar kungiyar PLO ta ce irin wadannan maganganu kokari ne na janye hankalin duniya daga kan abinda kwamitin ya bayyana a zama miyagun manyan laifuffukan da dakarun mamayar Isra'ila ke aikatawa.

Tun da farko a jiya lahadi, ministan harkokin wajen Masar, Ahmed Maher, ya ce kasarsa ta na bada cikakken goyon baya ga abinda ya kira gwamnatin Falasdinawan da aka zaba bisa tsarin demokradiya, sannan ya ce Masar tana kyamar duk wani matakin neman kewayawa ta bayan gwamnatin, a yi ban da ita.

XS
SM
MD
LG