Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil Ce Gagara-Badau - 2002-07-01


Brazil ta yi abinda ba a taba yi ba a fagen kwallon kafa ta duniya, inda a jiya lahadi ta lashe gasar cin kofin kwallon kafar a karo na biyar cikin tarihin fara irin wannan gasa.

Wasan wuta, da aka yi a daren jiya a birnin Yokohama na kasar Japan bayan da aka mikawa Brazil kofin gasar, ya haskaka sararin samaniyar wannan birni.

A wasan na karshe, Brazil ta doke Jamus da ci biyu da nema. Shararren dan wasan nan na Brazil, Ronaldo, shi ne ya antaya duka kwallayen biyu. Kazalika, Ronaldo ne ya cinye kyautar dan wasan da ya zarta saura a bajimtar cin kwallaye a gasar baki dayanta.

Ko bayan kasar Brazil, za a rika tuna gasar cin kofin kwallon kafar duniyar ta bana, a sakamakon bajimta da nasarorin da kasashe irinsu Senegal, Koriya ta Kudu, da Turkiya suka nuna, da kuma yadda 'yan kallo a Japan da Koriya ta Kudu, kasashen Asiya guda biyu da suka amshi bakuncin gasar, suka rika halartar filayen gasar kididi, cikin wata shiga ta musanman.

XS
SM
MD
LG