Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirage Biyu Sun Yi Karo A Sama A Jamus - 2002-07-02


Wani jirgin saman fasinja da na daukar kaya sun yi karo jim kadan kafin karfe goma sha biyun daren litinin a kusa da tabkin Constance dake kudancin Jamus, lamarin da ya watsar da gawarwakin mutane da tarkace a yanki mai fadin gaske.

Watakila kuma akwai wadanda suka mutu a kasa a sanadin wannan hadarin.

'Yan sanda da jami'an tsaro sun dukufa ka'in da na'in ga ayyukan binciken yankin, ta yin amfani da tocila da manyan fitilun da aka makala a jikin jiragen sama masu saukar ungulu.

Rahotannin farko sun ce jiragen biyu da suka yi wannan hadarin sun hada da wani jirgin daukar kaya kirar Boeing-757 da wani jirgin saman fasinja kirar Tupolev-154 wanda ya dauko fasinjoji daga tsohuwar Jamhuriyar Tarayyar Soviet ta Belarus.

Babu takamammen bayani na yawan mutanen da suka mutu, koda yake 'yan sanda sun bada rahotannin dake cewa watakila jirgin na Belarus yana dauke da mutane har 150, yayin da jirgin daukar kayan yake dauke da mutane biyu.

Wannan hadarin ya faru kusa da garin Ueblingen, amma kuma an samu tarkace da gawarwaki a warwatse a yanki mai fadin gaske. Wani rahoto ya ce an tsinci gawarwaki biyu a birnin Constance, aka kuma tsinci wasu da dama a filayen dake kusa da tabkin birnin.

Har yanzu babu takamammen bayani kan yadda aka yi wadannan jirage biyu suka yi karo, amma wani dan jaridar da ya gane wa idanunsa lamarin, ya fada ta gidan telebijin na Jamus cewa ya ga wuta kamar makeken kwallo ya tashi a sama, ya fado kasa kusa da tabkin Constance.

Ya ce gawarwaki sun warwatsu a filayen dake jikin tabkin, inda gawarwakin suka rika subutowa kasa daga nisan kilomita 12 ko 13 a sama.

XS
SM
MD
LG