'Yan sandan Afirka ta Kudu sun ce har yanzu suna farautar wasu barayin da suka fasa ofishin jakadancin Nijeriya dake birnin Pretoria a ranar litinin da daddare.
Hukumomi a Pretoria, sun fada jiya laraba cewa suna neman wadannan barayi su kimanin goma, wadanda suka danne masu gadin ofishin jakadancin na Nijeriya, suka nuna musu bindigogi, sannan suka shiga ciki suka kwashi abubuwan da zasu iya kwasa suka gudu.
Majiyoyin 'yan sanda sun ce daga cikin abubuwan da aka kwashe har da akwatunan telebijin, da akwatunan bidiyo, da injuna masu kwakwalwa, da kuma tsabar kudin da ba a bayyana yawansa ba.
Daga nan barayin suka shiga ofis-ofis a wannan gini suka yi kaca-kaca da wurin.
Hukumomi sun fara gagarumin bincike game da wannan lamarin.