Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alassane Ouattara Ya Ja Kunnen Hukumomin Ivory Coast... - 2002-07-04


Ana saura 'yan kwanaki kadan a gudanar da zabubbuka na gundumomi, shugaban 'yan hamayya na kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya gargadi jami'an gwamnati cewar idan har ba a sassauto da tsarin jefa kuri'a ba, kasar tana iya fadawa cikin fitina.

Wannan damuwa tasa ta biyo bayan wani sabon shirin da gwamnati ta bayyana kwanakin nan, cewar sai masu jefa kuri'ar dake da sabbin katunan shaida ne kawai zasu iya jefa kuri'unsu a zabubbukan gundumomi na wannan makon.

An ce duk 'yan kasar ta Ivory Coast da ba su karbi sabon katin shaidar da gwamnati ke bayarwa nan da ranar 7 ga wata ba, to ba zasu iya yin amfani da lasisin tuki ko takardar shaidar haihuwa a zaman shaida ba.

Ana sa ran cewa 'yan kasar Ivory Coast zasu zabi sabbin majalisun gundumomi 58 ranar lahadi, a wani bangare na zaben yankunan da za a yi a duk fadin kasar.

XS
SM
MD
LG