Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kokarin Ceton Rayukan Mutane, Wasu Suna Kokarin Satar Albasa - 2002-07-05


Jami'an Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun ce mutane akalla 22 suka mutu a lokacin da wani jirgin saman daukar kaya ya fadi alhamis a wajen birnin Bangui.

Jami'an kula da zirga-zirgar jiragen sama suka ce matuka jirgin sun nemi iznin yin saukar gaggawa, to amma sai suka kasa kaiwa ga hanyar saukar jirage, suka fadi a kusa da kogin Obangui dake gundumar Guitangola.

Abin takaici kuma, shaidu sun ce 'yan kwasar ganima sun yi caa a inda aka yi hadarin, suka sace albasar da wannan jirgi ya dauko yayin da ma'aikatan agaji suke kokarin neman wadanda suke da rai a cikin garewanin jirgin. An samo mutane biyu da rai, aka garzaya da su zuwa wani asibiti domin jinya.

Wannan jirgin ya kuma lalata wasu gidaje biyu, amma kuma ba a san ko akwai wani a kasa da ya jikkata lokacin da jirgin ya subuto ba.

Jami'an kula da zirga-zirgar jiragen sama suka ce wannan jirgin daukar kaya kirar Boeing-707 ya taso ne daga N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, a kan hanyar zuwa Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Kwango. Jami'ai suka ce kamfanin jiragen sama na "Prestige Airlines" shine ke tafiyar da wannan jirgi.

XS
SM
MD
LG