Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yasser Arafat Yayi Garambawul A Hukumomin Tsaron Falasdinawa - 2002-07-05


Jami'an Falasdinawa sun ce shugaban Falasdinawan, Yasser Arafat, ya kori babban jami'in tsaron kai a yankin Yammacin kogin Jordan, yayin da yake ci gaba da yin garambawul a hukumomin tsaron Falasdinawan.

Jami'an sun ce Malam Arafat ya rattaba hannu kan wata doka jiya alhamis, wadda ta cire Kanar Jibril Rajoub daga kan mukaminsa na tsaro, aka maye shi da gwamnan Jenin, Zuheir Manasrah. Suka ce shi kuma Rajoub yanazu zai koma ya rike mukamin na gwamnan Jenin.

Jami'an sun kuma ce babban baturen 'yan sanda na zirin Gaza, Ghazi jabali, ya mika takardar murabus dinsa.

Da farko, dukkan mutanen biyu sun musanta rahotannin da aka bayar talata cewa Malam Arafat zai kore su.

Amurka da Bani Isra'ila sun matsawa Malam Arafat lambar cewa lallai sai ya yi garambawul ga hukumomin tsaron Falasdinawa. Amma wasu masu fashin baki sun ce barin mukaman da Malam rajoub da Malam Jabali suka yi da alamun siyasa ce kawai.

XS
SM
MD
LG