Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pinochet Yayi Murabus Daga Majalisar Dattijai... - 2002-07-05


Tsohon shugaban gwamnatin kama-karya ta kasar Chile, Augusto Pinochet, yayi murabus daga kan kujerarsa ta mutu-ka-raba a majalisar dattijai, kwanaki uku a bayan da kotu ta ce babu dama a iya tuhumarsa da aikata wani laifi lokacin da yake mulki daga 1973 zuwa 1990.

Shugaba Ricardo Lagos ya bayyana fatan cewa murabus din da aka bada sanarwa jiya alhamis na Mr. Pinochet, zai kawo abinda ya kira kwanciyar hankali a kowane bangaren rayuwa na al'ummar kasar Chile.

A ranar litinin, kotun koli ta Chile ta yanke hukumcin cewa tsohon janar din mai shekaru 86 da haihuwa ba ya da cikakken hankalin tsayawa gaban shari'a.

An tuhume shi da laifin bada umurnin kamawa da gana azaba, tare da kashe dubban abokan adawar siyasa a hannun kungiyoyin 'yan daba, a bayan da ya kwace mulki a shekarar 1973 a juyin mulki na sojoji.

XS
SM
MD
LG