Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dan Agolar Saddam Hussein A Miami - 2002-07-05


Hukumomi a nan Amurka sun kama wani dan agolar shugaba Saddam Hussein na kasar Iraqi bisa zargin karya dokokin shige da ficen baki. Amma kuma jami'ai sun ce babu wata shaidar cewa yana da alaka da wata kungiyar ta'addanci.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, FBI, ta fada jiya alhamis cewar ranar laraba ta tsare Mohammed Saffi a birnin Miami, a Jihar Florida.

Jami'an hukumar ta FBI suka ce Mohammed Saffi, wanda injiniya ne na zirga-zirgar jiragen sama, yayi kokarin daukar darussan tukin jiragen sama, amma kuma ba ya da takrdar bizar da ake bukatar kowane dan kasar waje ya mallaka kafin ya shiga wata makarantar koyon tukin jirgin sama a nan Amurka.

Wata jaridar da ake bugawa a jihar ta Florida yayi kokarin shiga wata makarantar da daya daga cikin 'yan fashin jiragen sama na 11 ga watan Satumba ya shiga.

Jami'ai suka ce a bisa dukkan alamu abinda za a yi kawai shine maida Mohammed saffi zuwa kasar New Zealand, inda ya zamo dan kasa.

XS
SM
MD
LG