Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harbe-Harben Da Aka Yi A Filin Jirgin Saman Los Angeles Ba Ta'addanci Ba Ne - In Ji Hukumar FBI - 2002-07-05


Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya a nan Amurka, FBI, ta ce babu wata alamar cewa akwai hannun 'yan ta'adda a harbe-harben da aka yi jiya a filin jirgin saman Los Angeles, inda mutane uku suka mutu.

Wani dan bindigar da har yanzu ba a bayyana ko wanene ba, ya kashe mutane biyu a layin masu shiga jirgin kamfanin El Al na kasar Bani Isra'ila, kafin wani jami'in tsaron kamfanin ya bindige shi har lahira.

Hukumar FBI ta ce da alamun wannan lamari ne da ba zama aka yi a gungu aka kitsa shi ba. Hukumar ta FBI ta ce ba ta neman wani mutum dabam game da harbe-harben im ban da shi wannan dan bindiga shi kadansa.

Jim kadan a bayan harbe-harben na filin jirgi kuma, wani dan karamin jirgi ya fadi a wata unguwar dake bayangarin birnin Los Angeles, ya kashe mutane uku. Hukumar FBI ta ce babu wata alaka a tsakanin al'amuran biyu.

XS
SM
MD
LG