Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Da Iraqi Sun Kasa Daidaitawa, Yayin Da Afirka Ta Kudu ta Ce Tana Goyon Bayan Iraqi - 2002-07-06


Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya kasa shawo kan Iraqi domin ta kyale sufetocin majalisar su shiga kasarta domin farautar makaman da aka haramta mata mallaka.

Mr. Annan da wani babban jami'in gwamnatin Iraqi sun yi zagaye na uku na tattaunawa jiya Jumma'a a birnin Vienna. Tilas sai sufetocin majalisar sun tabbatar da cewa Iraqi ba ta mallaki makaman kare-dangi ba kafin a dage takunkumin cinikayyar da majalisar ta sanya mata.

Amma Iraqi ta ce tilas sai an warware wasu batutuwan tukuna, ciki har da barazanar da Amurka take yi ta hambarar da shugaba Saddam Hussein. An shirya yin tattaunawa ta hudu a tsakanin Mr. Annan da ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, amma kuma ba a tsayar da rana ba.

A halin da ake ciki, mukaddashin shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, yayi tur da takunkumin na MDD a kan Iraqi. A tattaunawar da yayi da mukaddashin firayim ministan Iraqi, Tariq Aziz, Mr. Zuma ya ce wasu kasashe 'yan cin zali suna tilastawa kungiyoyi na kasa da kasa, kamar MDD, yin aiki da muradunsu.

A bisa dukkan alamu, Mr. Zuma yana shagube ne da kasashen Amurka da Britaniya, wadanda suka shawo kan majalisar ta sanyawa Iraqi takunkumi bayan da ta kai harin mamaye Kuwait a shekarar 1990.

Mr. Zuma ya ce al'ummar Afirka ta Kudu suna matukar bakin cikin irin bakar wahalar da wannan takunkumin da aka kafa shekaru 12 da suka shige ya jefa al'ummar Iraqi a ciki.

Mataimakin shugaban na Afirka ta Kudu ya ce ba za a taba samun adalci ba yayin da kasashe 'yan cin zali suka mayar da mafi yawan sassan duniya saniyar ware, marasa abin cewa. Ya kara da cewa bai kamat wani bangare na duniya, ko nahiya ko kuma kasa ta bai wa kanta ikon yanke shawarar abinda kowa zai yi ba.

XS
SM
MD
LG