Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Kashe Mutane 36 Ranar Bukin Samun 'Yancin Kan Aljeriya - 2002-07-06


Bama-bamai akalla guda uku sun tashi, suka girgiza jama'a a Aljeriya, yayin da kasar ke bukukuwan cikar shekaru 40 da samun 'yancin kai daga hannun Faransa.

Bam mafi barna ya lankwame rayukan mutane 35, ya ji rauni ma wasu guda 80 a wata kasuwar sayar da kayan miya a garin Larbaa. Bam din ya tashi da safe, daidai lokacin da wannan kasuwa ta cika makil da masu yin cefane.

Wasu bama-baman sun tashi a bakin teku a wajen birnin Algiers, da kuma a yankin Jijel, inda mutum guda ya mutu.

Babu wanda ya dauki alhakin dasa bama-baman. Amma an yi ta fargabar cewa masu kishin addini zasu kai hare-hare lokacin bukukuwan.

XS
SM
MD
LG