Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jami'in MDD Ya Ce Al'ummar Angola Suna Cikin Tsananin Ukuba... - 2002-07-06


Wani babban jami'in MDD ya ce halin jinkai da ake fama da shi a kasar Angola har yanzu yana da tsananin gaske, amma kuma a yanzu ana ganin alamun cimma zaman lafiya fiye da kowane lokaci a baya.

Babban jami'in kula da ayyukan rarraba kayan agaji na gaggawa na MDD, Kenzo Oshima ya kammala ziyarar aiki jiya Jumma'a a kasar Angola, yana mai rokon da a bada agajin gaggawa ga miliyoyin 'yan kasar Angola wadanda ya ce suna zaune ciki ukuba.

Mr. Oshima ya ce duk da kyautatuwar tsaro sosai yanzu a kasar Angola, har yanzun ana bukatar agajin gaggawa daga kasashen waje domin shawo kan illolin da yakin basasar shekaru kusan 30 ya haddasa cikin kasar.

XS
SM
MD
LG