Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowane Bangare Yana Ikirarin Samun Nasara A Hukumcin Da Kotun Afirka Ta Kudu ta Yanke Kan Maganin Cutar AIDS - 2002-07-06


Dukkan bangarorin dake rikici da juna kan samar da maganin yakar cutar kanjamau ta AIDS a Afirka ta Kudu, suna ikirarin samun nasara, a bayan wani hukumcin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke jiya Jumma'a.

Dukkan alkalan kotun sun yarda da hukumcin da ya umurci gwamnati ta bada wani maganin dake yakar kwayar halittar HIV ga mata masu juna dake dauke da wannan kwayar cuta, a dukkan asibitocin gwamnati, ba wai a wurare guda 18 kawai da aka kebe ba.

Kotun ta ce takaita bada wannan magani mai suna "Nevirapine" ya take hakkin da tsarin mulki ya bai wa mata masu juna dake dauke da kwayar cutar HIV, da kuma jariransu.

'Yan rajin kare hakkin masu fama da cutar AIDS sun yaba da wannan hukumci, suna bayyana shi a zaman wanda ya nuna gaskiyar matsayinsu.

Ministan lafiya na Afirka ta Kudu ya amince da hukumcin, yana mai cewa ya tabbatar da fa'idar shawarar da gwamnati ta yanke cikin watan Afrilu na fadada rarraba maganin na Nevirapine a duk fadin kasar.

XS
SM
MD
LG