Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Kasashen Afirka Da Su Samar Da Ayyukan Yi Ga Mutane Miliyan 100 Cikin Shekaru 10 - 2002-07-07


Shugaban kungiyar kwadago ta kasa da kasa ya ce tilas batun samar da ayyukan yi ga jama'a ya zamo daya daga cikin manyan muradun kasashen Afirka, tun da za a bukaci sabbin ayyukan yi miliyan 100 cikin shekaru goma masu zuwa domin sabins higa aiki kawai.

A lokacin da yake magana a birnin Durban, a Afirka ta Kudu, darekta-janar na kungiyar ta ILO, Juan Somavia, ya shaidawa ministocin kasashen Afirka cewar samar da ayyukan yi wadatattu zai zamo wani mizani na tasirin sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka da za a kaddamar.

Ministocin na Afirka suna birnin Durban ne domin tsara taron kolin da za a fara gobe litinin, taron da a jibi talata zai kaddamar da Tarayyar Kasashen Afirka, wadda zata maye gurbin kungiyar Hada kan Kasashen Afirka ta OAU da aka kafa shekaru 39 da suka shige.

A jiya asabar, shugaba Mu'ammar Gaddafi na Libya yana daya daga cikin shugabannin da suka fara isa birnin Durban cikin gagarumin tsaro. Yana daya daga cikin jigogin kafa sabuwar tarayyar, wadda ya ce ya kamata a ba ta hurumin takalar fitinu a nahiyar.

Tun da fari, shi ma shugaba John Kufuor na Ghana ya isa birnin Durban, inda ake sa ran shugabannin kasashe fiye da 40 na Afirka zasu halarci kaddamar da sabuwar tarayyar. Shi ma babban sakataren MDD, Kofi Annan, yana kan hanyar zuwa wurin wannan taron koli.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambaci shugaban OAU mai barin gado, shugaba Levy Mwanawasa na Zambiya, yana fadin cewa Libya ta gabatar da tayin karbar bakuncin hedkwatar sabuwar tarayyar a cikin kasarta. Hedkwatar kungiyar OAU dai yana Addis Ababa, a kasar Ethiopia ne.

Mr. Mwanawasa ya ce taron kolin na Durban zai yanke shawara a kan ko za a kawar da hedkwatar daga Ethiopia.

XS
SM
MD
LG