Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Da Kwararru Dubu 14 Sun Hallara Domin Taron Duniya Kan Cutar AIDS - 2002-07-07


Likitoci da kwararru dubu 14 suna birnin Barcelona a kasar Spain, domin taron kasa da kasa na 14 kan cutar AIDS, a daidai lokacin da ake kara nuna damuwar cewa yanzu kam dai cutar yaduwa take kara yi.

Yau lahadi za a fara gudanar da wannan taro na mako guda.

Masu bincike kan cutar ta AIDS sun bukaci likitoci da su yi aiki da sabbin dabaru na yakar wannan cuta. Suka ce kwayar halittar cuta ta HIV mai haddasa cutar AIDS, ta fara jurewa magungunan da ake yin amfani da su a yanzu.

Har ila yau suka ce mutane sun fara yin sakaci da hanyoyin rigakafin kamuwa da cutar AIDS bisa imanin cewa za a iya warkar da wannan cuta cikin sauki.

Koda yake annobar cutar AIDS ta fi yin tsanani a nahiyar Afirka, kwararru sun ce a yanzu cutar ta fi yaduwa a kasashen dake gabashin nahiyar Turai.

Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa akwai mutane miliyan arba'in a fadin duniya da ko dai suna dauke da cutar ta AIDS ko kuma kwayar halittar cuta ta HIV mai haddasa ta.

XS
SM
MD
LG