Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Bukaci Da A Dauko Fansar Kashe Wata Mata Da 'Yar Jaririyarta - 2002-07-07


Dubban Falasdinawan dake halartar jana'iza a fusace sun yi kira ga 'yan ta-kifen Falasdinawa da su je su dauko fansa a kan Isra'ila saboda kisan wadannan mutane ad suka ce ta yi.

Mutane akalla dubu uku ne suka hallara jiya asabar a garin Khan Younis dake zirin Gaza domin jana'izar wadannan mutane biyu: wata mata da 'yarta mai shekaru biyu da haihuwa.

Jami'an asibiti na Falasdinawa sun ce an bude wuta kan matar da 'yarta a cikin motarsu kusa da wata unguwar yahudawa 'yan share ka zauna a zirin Gaza aka kashe su.

A halin da ake ciki, majiyoyin Falasdinawa sun ce jami'an tsaron Falasdinu su fiye da 100 sun ki yarda da matakin da Yasser Arafat ya dauka na maye gurbin tsohon jami'in tsaro Jibril Rajoub, da Zuheir al-Manasra, wanda a lokacin wannan canji yake rike da mukamin gwamnan Jenin.

XS
SM
MD
LG