Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tsammanin Sojoji Ravalomanana Zasu Kwace Sauran Sassan Madagascar - 2002-07-07


Nan da 'yan kwanaki kadan ake sa ran sojoji masu yin biyayya ga shugaba Marc Ravalomanana na kasar Madagascar zasu kwace sauran tungar da ta rage a hannun dakarun Didier Ratsiraka, tsohon shugaban kasar.

Rahotanni sun ce watakila a yau lahadi, ko kuma a gobe litinin sojojin zasu kaddamar da farmaki na karshe kan birnin Toamasina mai tashar jiragen ruwa a gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ce a jiya asabar sojojin suka kama shingayen da masu biyayya ga Mr. Ratsiraka suka kafa a kan hanya kimanin kilomita 100 a yamma da tungar tsohon shugaban.

Rahotanni sun ce sojojin gwamnati ba su tsammanin zasu fuskanci turjewa ko adawa mai tsanani a bayan da Mr. Ratsiraka ya gudu zuwa tsibirin Seychelles a ranar Jumma'a. Rahotanni sun ce ana tsammanin a yau lahadi zai tashi zuwa kasar Faransa.

Kasashe da dama, cikinsu har da Amurka da Japan da Australiya da kuma Faransa, sun amince da Mr. Ravalomanana a zaman shugaban Madagascar.

XS
SM
MD
LG