Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Tara Suka Mutu, Sanadin Ambaliyar Ruwa A Jihar Texas - 2002-07-07


Ruwan sama kamar da abkin kwarya da aka shafe mako guda ana yi, ya haddasa ambaliyar ruwan da ta kashe mutane da dama tare da janyo hasarar dukiya mai yawa a wasu sassan jihar Texas a nan Amurka.

Jami'ai sun ce wannan ruwan ambaliya a yankunan kudanci ad tsakiyar jihar ta Texas, ya kashe mutane akalla tara. Ala tilas, wasu mutane su dubu hudu sun gudu daga cikin gidajensu, gidajen da aka ce a yanzu wasu sai rufinsu kawai ake iya gani a saman ruwa.

Hukumomi sun ce wasu yankunan sun samu ruwan da ya zarce mita daya cikin makon nan kawai.

Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta ce a yanzu alamu na karuwa cewar ba za a sake zabga ruwan sama cikin 'yan kwanakin dake tafe a yankin ba. Shugaba Bush ya ayyana yankunan kananan hukumomi 10 a jihar tasu ta Texas a zaman wadanda bala'i ya shafa, matakin da zai iya sanyawa su samu agajin gwamnatin tarayya.

XS
SM
MD
LG