Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Za A Yi Taron Kolin Karshe Na Kungiyar OAU - 2002-07-08


A yau litinin za a yi zaman karshe na Kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka ta OAU, saboda daga gobe talata, kungiyar zata rikide ta koma Tarayyar Kasashen Afirka. Shugabannin kasashe daga kowane lungu na nahiyar sun yi caa a kasar Afirka ta Kudu domin wannan gagarumin taron koli da za a yi.

Wakiliyar Muryar Amurka a birnin Durban, ta ce shugabanni fiye da 40 daga kusan kowace kasa ta nahiyar Afirka, sun hallara a birnin na Durban, domin taron koli na 38 kuma na karshe na kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka ta OAU, tare da kaddamar da sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka. Shi ma babban sakataren MDD, Kofi Annan, yana can birnin na Durban domin wannan buki na tarihi.

Akidar Tarayyar Kasashen Afirka ita ce ta yakar talauci tare da kawo karshen rikice-rikice a fadin nahiyar Afirka. Jami'an huldar jakadanci da masu fashin baki sun ce tarayyar tana fatan yin gini bisa harsashin nasarorin da kungiyar OAU ta samu, yayin da zata yi kokarin kaucewa irin kura-kuran da ita OAU din ta yi a can baya.

Darekta Cibiyar Nazarin harkokin Tsaro dake Afirka ta Kudu, Jakkie Cilliers, ya ce za a samu madafar ci gaba, tare kuma da sauyi idan Tarayyar Kasashen Afirka ta maye gurbin Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka a gobe talata.

Mr. Cilliers ya kara da cewa, "...idan mutum ya dubi daftarin da ya kafa Tarayyar Kasashen Afirka, zai ga cewa ya kunshi akidojin da suka shafi kare hakkin Bil Adama da dimokuradiyya, abubuwan da babu su, ko miskala zarratin cikin daftarin da ya kafa kungiyar OAU. Amma kuma yin aiki da wadannan akidoji, zai zamo kalubale. Kuma ya kamata mu fahimci cewa babu wata hanya mai sauki ta warware matsalolin rashin kwanciyar hankali da rashin ci gaba a nahiyar Afirka. Wannan sauyi ne da sai an shafe shekaru masu yawa kafin a ga amfaninsa. Abinda kawai zan iya cewa shine: a yanzu, Afirka ta doshi alƙibla mai kyau, sannu kan hankali."

A jiya lahadi, kwana guda kafin taron kolin na karshe na kungiyar OAU, an yi ta gudanar da kananan tarurruka kan batutuwa dabam-dabam.

Shugabannin Afirka su akalla 10 sun gana domin tattauna sabon Kawancen Raya Tattalin Arzikin Afirka, wanda aka fi sani da sunan NEPAD. Wannan shiri, shine zai zamo tamkar babbar manufar tattalin arziki ta Tarayyar Kasashen Afirka. Shirin NEPAD ya tanadi cewa kasashen Afirka zasu rungumi akidar yin mulkin adalci da gaskiya tare da bin tafarkin dimokuradiyya. Idan sun yi hakan kuma, suna son kasashe masu arzikin masana'antu su zuba jarurruka cikin Afirka su kuma bunkasa huldar cinikayya, maimakon mikawa kasashen na Afirka agaji.

Akasarin shugabannin da suka halarci wannan taro na NEPAD a birnin Durban masu goyon bayan shirin ne. Amma kuma, shi ma shugaban kasar Libya, Mu'ammar Gaddafi, wanda ya nuna adawa da shirin a can baya, ya halarci wannan taro. Majiyoyi sun ce a bayan wata ziyarar da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya kai masa a makon da ya shige, shugaba Gaddafi, a bisa dukkan alamu, ya yarda cewa zai amince da wannan shiri na NEPAD, ko kuma dai ba zai fito yayi adawa da shi ba.

XS
SM
MD
LG