Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Taron Kasashen Duniya Kan Cutar AIDS a Spain - 2002-07-08


Taron shekara shekara na 14 kan cutar kanjamau ta AIDS ko SIDA da aka fara a birnin Barcelona a kasar Spain, shine mafi girma da aka taba yi, yayin da a gefe guda ake nuna damuwar cewa cutar tana yaduwa gadan-gadan.

Mutane fiye da dubu 14, wadanda suka hada da likitoci da kwararru da masu bincike da kuma 'yan rajin kare hakkin masu fama da cutar, suke halartar wannan taron mako guda da zai mayar da hankali kan wayar da kawunan jama'a game da cutar AIDS, da kuma kudurin daukar matakan dakile yaduwar cutar da hana mutane kamuwa da ita.

Darektan Shirin Yakar Cutar AIDS na Majalisar Dinkin Duniya, Peter Piot, ya bude taron jiya lahadi yana mai cewa duk da wayewar kai game da wannan cuta, da kuma kudurin shugabannin siyasa, har yanzu kudin da ake samarwa ga kokarin yakar cutar bai kai yadda ake bukata ba.

Mr. Piot ya ce kasawar da shugabannin duniya suka yi wajen fahimtar irin barazana ta zahiri da cutar AIDS ke yi, ta taimaka wajen kara yaduwar annobar cutar.

Shaihin malami a fannin aikin likita a Jami'ar Barcelona, Jose Maria Gatell, wanda ke halrtar wannan taro, ya shaidawa Muryar Amurka cewa a yanzu masu bincike suna gabatar da sabbin magunguna na yakar kwayar halittar cuta ta HIV. Amma kuma ya kara da cewa samar da magani mai rahusa ga wadanda suke bukata, yana da matukar muhimmanci.

XS
SM
MD
LG