Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Binne Mataimakin Shugaban Afghanistan Da Aka Kashe - 2002-07-08


An binne mataimakin shugaban kasar Afghanistan, Haji Abdul Qadir, jiya lahadi a birnin Jalalabad dake gabashin kasar, yayin da aka fara binciken yadda aka yi aka kashe shi.

Haji Abdul Qadir shine babban jami'in gwamnati na biyu da aka kashe cikin wannan shekara a Afghanistan.

A ranar asabar wasu 'yan bindigar da suka yi shigar masu gadi suka bindige Haji Abdul Qadir har lahira tare da direbansa a kofar ofishinsa a birnin Kabul.

Dubban jama'a suka yi layi dauke da makarar tsohon shugaban daga wani babban Masallaci a Jalalabad zuwa wurin da aka yi masa kabari a tsakiyar birnin.

Shugaba Hamid Karzai ya ce zai nemi taimakon kasashen waje wajen binciken kashe mataimakin shugaban, idan har masu bincike na Afghanistan suka kasa gano wadanda suka kashe shi.

XS
SM
MD
LG