Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaddafi Yana Rangadi Cikin Mota - 2002-07-12


Shugaba Mu'ammar Gaddafi na Libya, ya isa 'yar karamar daular nan ta Swaziland dake yankin kudancin Afirka tare da wata makekiyar tawaga, bayan da ya taimaka wajen kaddamar da sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka a cikin makon nan.

Jiya alhamis Kanar Gaddafi ya isa fadar sarkin kasar a Ludzidzini tare da motoci kusan 100 wadanda harsashi ba ya ratsa su, kuma tare da zaratan 'yan mata masu gadi. Sarki Mswati na kasar Swaziland ya tarbe shi, inda aka yi masa fareti ya kuma kalli wasannin gargajiya.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce 'yan kasar ta Swaziland masu kaunar shugaba Gaddafi sun wuni suna ta rerawa da kiran sunansa kawai.

Kamfanin dillancin labaran ya ce a lokacin da suka zo wuce wasu bukkokin da suka rurrushe, shugaba Gaddafi ya tsayar da motocinsa a wurin. Yayi alkawari ma wata matar da ya gani a cikin wata bukka cewar in Allah Ya yarda kakarta ta yanke saka.

Gobe asabar Kanar Gaddafi yake shirin wucewa zuwa kasar Mozambique.

Wasu suna sukar shugaban na Libya da shi kansa Sarki Mswati wanda ya haramta jam'iyyun adawa a kasarsa, da laifin dakushe yaduwar mulkin dimokuradiyya, babban abinda sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka take kwadayin yadawa.

XS
SM
MD
LG