Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Sakatarori Hudu Sun Goyi Bayan Kafa Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida - 2002-07-12


Wasu sakatarori hudu 'yan majalisar zartaswa a gwamnatin shugaba Bush sun shaidawa majalisar dokoki cewar suna goyon bayan kafa ma'aikatar tsaron cikin gida da shugaban ya bada shawarar kafawa.

Sakataren harkokin waje Colin Powell, da atoni-janar John Ashcroft, da sakataren Baiyulmali Paul O'Neill, da kuma sakataren tsaro Donald Rumsfeld, sun bayyana jiya alhamis a gaban 'yan majalisar dokoki, wadanda suke aiki kan kudurin kafa sabuwar ma'aikatar.

Sakatarorin hudu sun ce sabuwar ma'aikatar zata hada kan muhimman ayyukan da ake bukata domin hana abkuwar ta'addanci. Har ila yau sun ce al-Qa'ida ta nan da rai a cikin Amurka, kuma a shirye take ta kai wani harin.

Shugaba Bush ya ce yana fatan sanya hannu a kan dokar kafa sabuwar ma'aikatar kafin ranar cikar shekara guda da hare-haren ta'addancin na 11 ga watan Satumba.

XS
SM
MD
LG