Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Gwabza Da Kiristoci Mabiya Darikar Katolika A Ireland Ta Arewa - 2002-07-13


'Yan sanda a Ireland ta Arewa sun gwabza da 'yan zanga-zanga mabiya darikar Katolika a karshen faretin da kiristoci mabiya darikar Protestant masu goyon bayan ci gaba da mulkin Ingila suka yi.

Kiristoci 'yan katolika amsu kishin kasa a bangaren arewacin birnin Belfast, sun jefa bama-baman fetur da kwalabe, da duwatsu da tubalai kan 'yan sanda da daruruwan 'yan darikar Protestant dake komawa gida daga faretin jiya Jumma'a.

'Yan sanda sun harba harsasan roba a yayin da suke kokarin shiga tsakanin bangarorin guda biyu. An raunata 'yan sanda da fararen hula da dama.

Dubban kiristoci 'yan darikar Protestant sun shiga cikin wannan faretin mai suna "Orange Order Parade", wanda ake yi a birnin na Belfast a kowace shekara domin murnar nasarar da 'yan Protestant suka samu kan sojojin Sarki James na Biyu dan darikar katolika a shekarar 1690.

'Yan Katolika suna daukar wannan fareti da ake yi ta cikin unguwanninsu a zaman maras amfani, kuma na neman tsokana kawai.

XS
SM
MD
LG