Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rahoto Yace China Tana Mika Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Ga Kasashen Da Ake Zargin 'Yan Ta'adda Ne - 2002-07-13


Wata hukumar da ta kunshi dukkan jam'iyyu wadda majalisar dokokin Amurka ta kafa, ta ce China tana gurgunta tsaron kasa na Amurka ta hanyar sayar da fasahar kera makamai masu linzami ga kasashen da ake zargin suna goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Wannan rahoton da Hukumar Nazarin Tsaron Amurka da China ta bayar jiya Jumma'a, ta ce kasar China tana yin amfani da rarar cinikayya mai yawa da take samu kan Amurka wajen biyan kudin gudanar da manufofin da suka sabawa muradun Amurka.

Manufofin sun hada da sayarwa da kasashe kayayyakin da za a iya yin amfani da su wajen harhada makaman kare dangi, da kuma kokarin da China ta dukufa ga yi, ciki har da leken asiri, domin samo sabbin fasahar kera makamai na Amurka.

Rahoton ya ce manufofin Amurka ya kasa hana kasar China kokarin mallakar fasahar kera makamai ta zamani.

Har yanzu hukumomi a birnin Beijing ab su ce uffan ba game da rahoton.

XS
SM
MD
LG