Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukin Dandalin Soyayya Na Bana Yayi Armashi A Birnin Berlin... - 2002-07-14


Dubun dubatan 'yan shagli da holewa sanye da tufafin da kusan za a ce bai rufe komai ba, sun yi ta rawa jiya asabar a titunan birnin Berlin, a lokacin bukin shekara-shekara na 14 na Dandalin Soyayya a babban birnin na Jamus.

Jami'an 'yan sanda sun yi kiyasin cewa mutane dubu dari biyar, ko rabin miliyan ne suka fito domin wannan fareti na jiya inda a bisa al'ada aka yi ta rusa kade-kaden turawa na zamani da ake kira Techno. Wadanda suka shirya bukin, sun sa ran cewa mutane fiye da haka zasu fito, amma kuma adadin na bana ya nuna yadda yawan masu halartar bukin ke ja da baya, tun lokacin da mutane miliyan daya da rabi suka halarci Dandalin Soyayyar 1999, suka haddasa mummunan cunkoson motoci a birnin.

Tsoron 'yan ta'adda ya sa wasu da yawa sun yi zamansu a gida, amma an yi wannan buki lami lafiya.

Bukin Dandalin Soyayya na farko da DJ Dodctor Motte ya shirya a shekarar 1989, ya samu halartar mutane 150 ne kacal, amma a cikin 'yan shekarun nan, mutane fiye da miliyan guda ne suke halartarsa.

XS
SM
MD
LG