Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoma A Kasar Mexico Sun Damke Karin Mutane Suna Yin Garkuwa Da Su A Ci Gaba Da Rikici Kan Batun Filin Jirgin Sama - 2002-07-14


Manoman kasar Mexico dake dauke da bama-bamai hadin gida, da adduna, sun kara damko wasu mutanen uku suka hada da wadanda suke yin garkuwa da su, a ci gaba da rikicin da ake yi kan shirin gwamnati na kwace filayensu domin gina sabon filin jirgin sama kusa da birnin Mexico City.

Manoman sun killace kansu cikin wani dan karamin gari dake dab da babban birnin kasar. A yanzu, wadannan manoma suna rike da mutane 15 suna yin garkuwa da su, sun kuma yi barazanar cewa zasu kona su da rai muddin 'yan sanda suka yi kokarin kwato su.

Manoman suna bukatar gwamnati da ta yi watsi da shirin kwace musu gonaki domin gina sabon filin jirgin saman da zai maye gurbin na yanzu wanda ya tsufa ainun a Mexico City.

Gwamnati ta ce zata biya manoman diyyar filayensu. Amma wasu manoman sun ce ko nawa za a ba su, ba zasu sayar da filayensu ba.

XS
SM
MD
LG